Bangladesh ta kama jagoran 'yan bindigar kabilar Rohingya
March 19, 2025Talla
Hukumomin 'yan sanda a Dhaka, babban birnin Bangladesh sun sanar a ranar Talata cewa sun tsare Ataullah Abu Ammar Jununi, jagoran kungiyar 'yan bindiga ta Arakan Rohingya Salvation Army ko kuma ARSA a takaice, bisa zargin aikata kisan kai da yi wa kasarsu zagon kasa.
A karkashin jagorancinsa ana zargin kungiyar ta ARSA da kaddamar da kazamen hare-hare kan shingayen jami'an tsaron kasar Myanmar a shekara ta 2017. Wadannan hare-haren ne kuma ake tunanin suka sabbaba sojojin Myanmmar kaddamar da samame dabam-dabam da suka tilasta wa Musulmai 'yan kabilar Rohingya sama da 750,000 tserewa daga kasar zuwa Bangladesh.