Bangladesh et Pakistan sun dinke zaman tankiya
August 24, 2025Bangladesh da Pakistan da suka dade suna zaman tankiya tun bayan raba kasashen biyu a 1971 sun amince a wannan Lahadi da karfafa dangantaka a tsakaninsu musamman a fannin tattalin arziki.
Duk da rashin neman afuwa daga bangaren Pakistan kan zaluncin da ta aikata wa 'yan Bangladesh a lokacin yakin neman 'yancin kai da suka gwabza, kasashen biyu sun rattaba hannu kan wata yarjejeniya domin karfafa mu'amala a fegen al'adu da kasuwanci inji Mohammad Touhid Hossain mashawarci a ma'aikatar diflomasiyar Bangladesh a yayin hira da ya yi da manema labarai.
Manazarta dai na ganin cewa Indiya da ta gwabza dan karamin yaki na kwanaki hudu da Pakistan a cikin watan Mayu da ya gabata, za ta saka idanuwa sosai kan wannan dinke baraka da kasashen biyu suka yi a tsakaninsu, saboda sanhi da alakarta ta yi da Bangladesh a watan Ogustan bara.