Mataimakiyar sakatare janar na Majalisar Dinkin Duniya Amina J. Mohammed ta yi kira ga karin tallafi a bangaren ilimin mata a Afirka, domin su cimma gajiyar tsarin kasuwanci mara shinge na kasashen Afirkan.
Mataimakiyar sakatare janar na Majalisar Dinkin Duniya Amina Mohammed Hoto: picture-alliance/empics/B. Lawless
Talla
A wata hira da ta yi da wakilinmu na Yamai fadar gwamnatin Jamhuriyar Nijar Mahaman Kanta a gefen taron kungiyar Tarayyar Afirka AU, Amina J. Mohammed da kuma ke zaman 'yar siyasa daga Tarayyar Najeriya, ta yaba da tsarin kasuwanci mara shingen da kasashen Afirkan suka kaddamar tare kuma da bukatar gaggauta tallafawa ilimin yara mata.