Majalisar Dinkin Duniya ta bayyana cewa adadin bakin hauren da ke kokarin shiga Turai ba bisa ka'ida ba da suka mutu ko suka bace ya haura na bara har sau uku, tana mai cewa wajen ya zama makabartar kananan yara.
Sau da dama bakin hauren kan yi amfani da rubabbun kwale-kwale wajen shiga TuraiHoto: Borja Suarez/REUTERS
Talla
Hukumar Kula da Ilimin Kananan Yara ta Majalisar Dinkin Duniya UNICEF, ta nunar da cewa tsakanin watan Yuni da Agustan bana kadai kimanin mutane 990 da ke kokarin shiga Turai ne ko dai suka mutu ko suka bace, idan aka kwatanta da 334 da aka samu a shekarar da ta gabata ta 2022.