Baki miliyan daya sun fice daga Amurka saboda Trump
August 8, 2025Talla
Sakatariyar harkokin tsaron cikin gida ta kasar, Kristi Noem ta ce baki fiye da miliyan daya ne suka mayar da kansu kasashensu na asali ta hanyar amfani da wata manhaja da ma'aikatar ta samar.
Karin bayani: Amurka ta fara tesa keyar bakin haure zuwa gida
A cewarta daga watan Janairu zuwa yanzu an kama dubbun dubanta bara gurbin baki a kasar yayin da ba a samu rahoton shigar bakin haure cikin kasar a watanni uku da suka gabata ba.
Kristi ta kara da cewa, wannan ne karon farko a tarihin kasar da aka taba ganin irin wannan tsaron a iyakar kasar. Tun a lokacin yakin neman zabe ne dai Shugaba Trump ya sha alwashin korar baki marasa cikakkun takardun shaidar zama a kasar.