'Bajamushen da ya kashe mutane na fama da larurar kwakwalwa'
March 4, 2025Babban mai shigar da kara a birnin Mannheim na Jamus ya fada cewa an samu kwararan hujjoji da ke nuna cewa mutumin da ya far wa dandazon mutane da motaa birnin ya na fama da lalurar kwakwalwa.
Mutumin wanda yanzu haka ke kwance a asibiti tare da raunuka na fuskantar bincike da tuhumar kisa da kuma yunkurin kisa a cewar mai shigar da karan Romeo Schüssler.
'Dan Afghaninstan ya raunata mutane kusan 30 da mota a Jamus
Mutane biyu sun rasu sannan wasu sun samu raunuka bayan Bajamushen mai shekara 40 ya afka da motarsa kan jama'a a ranar Litinin a birnin na Mannheim da ke kudu maso yammacin Jamus.
Hukumomi sun fada cewa babu tabbacin mutumin ya yi hakan ne saboda dalilai na siyasa.
Maharin birnin Munich ya amsa laifinsa
Ko da yake shugaban rundunar 'yansandan birnin Ulrike Schäfer ya ce mutumin ya tuka motar ce kai tsaye kan mutanen da ya ke so ya take.