Baerbock za ta kai ziyara Najeriya
December 19, 2022Talla
A ranar farko ta ziyarar kwanaki biyu da zata kai yankin yammacin Afirka, Baerbock zata kai ziyara sansanin tsofaffin mayakan da kuma magoya bayan kungiyar Boko Haram da ke birnin Maiduguri, inda aka sauya musu tunaninsu. Kana zata ziyarci kauyukan da suka fuskanci hare-hare masu tada kayar baya a shekarar 2015.
Manufar ziyararta karkashin shirin Jamus na bayar da tallafin sake gine makarantu da asibitoci da kuma ofisoshin 'yan sanda shi ne, a bai wa al'umma damar komawa garuruwansu na asali da kuma samun ababen more rayuwa.