Wane ne zai maye gurbin Adeshina a bankin AfDB?
May 27, 2025Yin amfani da babban jari domin ci gaban nahiyar Afirka. Wannan shi ne taken taron shekara-shekara na Bankin Raya kasahen Afirka (AfDB) ko BAD a hukumance.wanda ke da manufofin karfafa zuba jari daga waje da cikin nahiyar domin ci gaban tattalin arziki. Hakan ya yi daidai da manufofin ci gaba mai dorewa, na yarjejeniyar Paris, da jadawalin kungiyar Tarayyar Afirka a kan manufofin tattalin arziki
Kasashe 81 mambobi na tattaunawa domin duba ayyukan bankin a cikin shekarar da ta gabata tare da daukar sabbin manufofi na gaba.
Wannan taro na shekara-shekara yana haɗe da taron shekara-shekara na kwamitin zartarwa bankin na AfDB da na kwamitin zartarwar Asusun Raya kasahen Afirka na FAD.
Haka kuma 'yan kwamitin zartarwar AfDB su 81 za su zabi sabon shugaban bankin na tsawon shekaru biyar, wanda zai maye gurbin Akinwumi Adesina dan Najeriya, wanda wa'adinsa na biyu zai kare a karshen watan Agusta.
'Yan takara biyar ne ke neman maye gurbinsa. A kwai Sidi Ould Tah dan kasar Mauritaniya, da Abbas Mahamat Tolli na Chadi, da Tshabalala Bajabulile Swazi yar Afirka ta Kudu, da Samuel Munzele Maimbo na Zambia da Amadou Hott na Senegal.
Da yake jawabi kan shekaru goma da ya yi yana shugabancin bankin, Akinwumi Adesina ya ce a karkashin jagorancinsa, bankin AfDB ya fi mayar da hankali ne kan bunkasa tattalin arziki da zamantakewa.
Ya ce duk da guguwar da Afirka ta fuskanta a duniya ta hauhawar farashin kayayyaki, amma kuma ta fuskar hauhawar basussuka da faduwar darajar kudi, da kuma sauyin yanayi, Afirka na ci gaba da nuna ci gaba mai dorewa.‘‘
A cewar bankin na AfDB, goma sha daya daga cikin kasashe ashirin da suka fi saurin bunkasar tattalin arzikin a duniya a shekarar da ta gabata, sun kasance a Afirka,
An kafa bankin ke ne da cibiyar ke a birnin Abidjan a ranar 10 ga Satumba, na shekara ta 1964
A cikin shekaru 60 ,jarin bankin ya karu daga miliyan 250 zuwa dalar Amurka biliyan 318
Sai dai tun bayan hawan Donald Trump kan karagar mulki a watan Janairun shekara ta 2025, Amurka, wadda ita ce kasa mafi yawan masu ba da taimako a bankin, ta yi barazanar janye gudummawar da take bai wa Asusun Raya kasahen Afirka, wato AfDB.
A cikin kudirin kasafin kudinta na shekarar ta 2026, fadar White House ta sanar da dakatar da tallafin da ta yi kiyasin dala miliyan 555 da ta ke bai wa bankin na BAD abinda zai iya zama babban cikas wa bankin