SiyasaTurai
Babban Bankin Turai ya rage kudin ruwa
January 30, 2025Talla
Ragin kudin ruwan wanda tuni aka tsammaci bankin zai yi shi ne karo na hudu a jere da bankin ke rage kudin ruwa.
Babban bankin Turan na yin sara yana duban bakin gatari wajen rage kudin ruwan don bayar da dama ga masu bukatar karbar bashi a banki.
Sai dai kuma duk da cewa matakin na iya habaka ci gaba, a waje guda kuma yana iya haifar da tsadar kayayyaki.