Babban bankin Turai ya amince ya saye takardun shaidar hanayen jarin Italiya
August 6, 2011Babban bankin Turai ya amince ya fara sayen takardun shaidar hanyen jarin ƙasar Italiya daga ranar Litini mai zuwa biyo bayan alƙawarin da gwamnati ta yi na gaggauta aiwatar da sauye sauyen rage giɓin kasasfin kuɗinta. Da farko a ranar Juma'a firaministan Italiya Silvio Berlusconi ya ba da sanarwar cewa ƙasarsa za ta gaggauta aiwatar da matakan tsuke bakin aljihu domin daidaita kasafin kuɗinta kafin shekara ta 2013 maimakon shekarar 2014. A makonnin baya bayan nan darajar takardun shaidar hannayen jarin Italiya ta faɗi bayan da masu zuba jari suka juya mata baya saboda ɗinbim bashin dake kan ƙasar da rashin bunƙasar tattalin arziki da kuma rikicin dake cikin gwamnati. Kwamshinan kula da harkokin tattalin arzikin tarayyar Turai Olli Rehn ya yi ƙoƙari kwantar da hankulan kasuwannin hannayen jari da cewa Italioya da Spain ba sa bukatar wani tallafi.
Ya ce: "Kasuwanni ba su farfaɗo ba kamar yadda muka yi fata daidai da matakan da shugabannin ƙasashe masu amfani da kuɗin Euro suka amince da su a ranar 21 ga watan Yuli. To sai dai babu hujjar yaɗa fargaba a kasuwannin hada-hadar hannayen bisa wani tsari na tattalin arziki."
Da yammacin jiya shugabannin ƙasashen Faransa, Jamus da kuma Spain sun tattauna ta wayar tarho game da matsalolin bashin na Turai.
Mawallafi: Mohammad Nasiru Awal
Edita: Zainab Mohammed Abubakar