SiyasaIsra'ila
Harin Isra'ila a Doha a kan Hamas
September 9, 2025Talla
A cewar wani jami'in Hamas wanda ya bukaci a sakaya sunansa, Israila ta kai hari kan tawagar Hamas da ke halartar taron neman sulhu da ake yi a birnin Doha, inda suke tattaunawa kan shawarar shugaba Donald Trump na tsagaita wuta a Gaza.
Kawo yanzu dai ba a bayyana ko jami'an da aka kai wa hari a Doha sun mutu ko kuma sun tsira .Kasashen duniya dai na ci gaba da yin Allah wadai da hare-haren na Isra'ila a Doha.