Ayatollah Khamenei ya ce Iran ba ta neman mallakar nukiliya
March 12, 2025Jagoran juyin juya halin Musulunci na Iran Ayatollah Ali Khamenei ya bayyana cewa kasarsa ba ta mallaki makaman kare dangi ba, kuma ba ta neman mallakansa. Wannan furucin na zama tamkar martaki ne ga shugaban Amurka Donald Trump wanda ya aike da wata wasika zuwa Teharan inda ya bukaci a tattauna kan shirin nukiliyar Iran. A lokacin wata ganawa da dalibai a birnin Teheran, Ayatollah Khamenei ya ce idan har Iran na son kera makaman nukiliya, Amurka ba za ta iya hana ta ba.
Sannan jagoran Musulunci na Iran ya yi imanin cewar tattaunawar nukiliya da Amurka ba za ta dage takunkumin da aka kakaba wa Iran ba. Kazalika Ayatollah ya ce barazanar matakin sojan Amurka a kan Iran ba shi da wani gurbi a halin yanzu. Sai dai kasar Sin ta sanar ta karbar bakuncin wakilan Rasha da Iran a birnin Beijing a ranar Juma'a, domin gudanar da wani taro kan batun nukiliyar kasar Iran.