Aung San Suu Kyi za ta fara yin ziyara a Turai
June 13, 2012Talla
Jagorar 'yan adawa ta ƙasar Bama Aun San Suu Kyi na shirin fara wani rangandi a cikin ƙasashen nahiyar Turai.Ziyara ta makonnin biyu wacce akanta Suky za ta isa a ƙasashen Sweden,da Nowai da Irland da Ingila da kuma Faransa
An shirya Missis Asan Su Kyi za ta biya a birnin Oslo inda za ta karɓi lambar yabo ta girma ta NOBEL da aka bata tun a shekara ta 1991,dangane da fafatukarta, ta tabbata da dimokaradiyya a Bama wacce bata karba ba a lokacin saboda ana yi mata ɗaurin talala.Hukumomin Bama sun saketa a shekara ta 2010 ,kuma a yanzu ta na riƙe da matsayin yar majalisar dokoki.
Mawallafi : Abdourahamane Hassane
Edita : Abdullahi Tanko Bala