SiyasaAfirka
Ko martanin Tarayyar Afirka zai yi tasiri ga Trump?
June 5, 2025Talla
Cikin wata sanarwa da kungiyar Tarayyar Afirka AU ta fitar ta nunar da cewa, matakin na Shugaba Donald Trump ka iya yin mummunan tasiri a kan alaka tsakanin al'ummomi da fannin musayar ilimi da huldar kasuwanci da alakar diplomasiyya wadda aka jima ana mutumta juna da ita shekara da shekaru tsakanin Amurka da Afirkan.