AU ta yaba da zaman sulhu tsakanin DRC da Ruwanda a Qatar
March 19, 2025Kungiyar Tarayyar Afirka ta nuna gamsuwarta kan tattaunawar sulhun da shugabannin kasashen Ruwanda da Jamhuriyar Dimokuradiyyar Kwango suka gudanar a birnin Doha na kasar Qatar.
Karin bayani:M23 ta zargi DRC da yin wasa da tattaunawar zaman lafiya
Qatar kasar dai ta fitar da sanarwar bazata inda ta ce ta jagoranci tattaunawa tsakanin Paul Kagame na Ruwanda da takwaransa na Kwango, duk da cewa Qatar bata fitar da cikakken bayani kan batun tsagaita bude wuta da kuma yarjejeniyar da aka cimma ba.
Karin bayani:Mutane 63,000 sun tsallaka Burundi daga DRC
Yakin da ake gwabzawa tsakanin 'yan tawayen M23 da ke samun goyon bayan Ruwanda da kuma sojojin Kwango a kasar da ke da arzikin ma'adinai ya yi sanadiyyar mutuwar mutane da dama. A baya bayan nan M23 ta kwace biranen Goma da Bukavu daga hannun dakarun gwamnatin Kwango.