Atiku ya raba gari da PDP
July 16, 2025Wata sanawar da tsohon mataimakin shugaban kasar ya fitar dai ya ce 'yan leman sun raba gari da manufofin kafa jam'iyyar tun daga farkon fari.
Tun daga farkon na watan nan ne dai dama aka kalli Atikun cikin wani taron kaddamar da sabuwar jam'iyyar ADC da ke zaman mattatara ta masu adawa a kasar. Kafin sanarwar da ofishinsa ya fitar da yammacin yau (Laraba) din nan da kuma tabbatar da rawar da ya ke shirin takawa a cikin sabuwar gwagwarmayar neman kare ikon na masu tsintsiya.
Karin bayani: ADC: Sabuwar alkiblar adawa a Najeriya
Duk da cewar dai an dade ana zaman jiran tsammani, daga dukka na alamu barin cikin gidan 'yar leman a banagre na Atikun na iya tasiri a cikin PDP da ke fuskantar rikicin cikin gida a halin yanzu. Akwai dai tsoron Atikun na iya dibar magoya bayan da ke da daman gaske cikin gidan 'yan lemar ya zuwa ga sabuwar jam'iyyar.
Karin bayani: Ko hadakar jam'iyyun adawa ne mafitar Najeriya?
Sau dai dai har uku ne dai tsohon mataimaki na shugaban kasar ya fice cikin gidan PDP ya zuwa jam'iyyu daban daban. A shekara ta 2007 ne dai Atikun ya bar gidan PDP ya zuwa jam‘iyar AC tare da yi mata takara ta shugaban kasa, kafin ya sake komawa cikin gidan jam'iyyar.
Karin bayani: Najeriya: Kokarin kafa jam'iyyar ADA don kalubalantar APC a 2027
Atikun ya sake ficewa a shekara ta 2014 tare da taka rawa a zabe na fid da gwanin jam'iyar APC kafin sabuwar ficewar da daga dukkan alamu ke iya sauya da dama cikin fagen na siyasa. Faruk BB Faruk dai na sharhi cikin fagen na siyasa, kuma ya ce ficewar tsohon mataimaki na shugaban kasar na shirin sauya rawar 'yan lema daga jam'iyyar da ke zaman ta kan gaba cikin gidan na adawa ya zuwa yar auta a tsakanin manya.
Atikun dai ya kafa tarihin zama na kann gaba cikin batu na takara a tarayyar Najeriya. Tun daga SDP daga farkon fari ya zuwa PDP yanzu haka ,sau dai dai har shida ne dai a tsakanin shekara ta 1993 zuwa ta 2023 Atiku Abubakar ke tsayawa takara ta shugabancin tarayyar Najeriya a karkashin inuwar jam'iyyu daban daban.