Assimi Goita ya rusa kungiyoyi da jam'iyyun Siyasa a Mali
May 13, 2025Gwamnatin mulkin sojin Mali ta rusa jam'iyyu da kungiyoyin siyasa na kasar, bayan kwashe makonni na fargaba daga wadanda matakin ya shafa. Dama dai tun da hantsin ranar Talata, hukumomin da ke jan ragamar Mali tun bayan juyin mulkin 2020 da 2021, sun fara soke kundin da ya tsara hanyoyin kafa jam'iyyun siyasa da yadda suke gudanar da ayyukansu da kuma hanyoyinsu na samun kudaden shiga.
Karin bayani: Zargin take hakkin dan Adam a Mali
Wannan matakin ya biyo bayan shawarwarin da aka tsayar a babban taro na kasa da aka yi a karshen watan Afrilu a Mali, wanda ya ce a ruguza jam'iyyu tare da tsaurara matakan kirkiro wasu sabbi. Sannan ya ba da shawarar ayyana Janar Assimi Goïta, a matsayin shugaban kasa na wa'adin shekaru biyar ba tare da zabe ba, lamarin da ya yi hannun riga da alkawarin da ya yi na mika wa farar hula mulki a watan Maris na 2024. Tuni dai 'yan adawa da dama na kasar Mali suka fura cin karo da mataki na shari'a daga hukumomi, duk da matsalar tattalin arziki da kalubalen tsaro da kasar ke fuskanta.