Tanzaniya: Beraye da gafiyoyi na taimako?
September 4, 2025Wadannan gafiyoyi da beraye na musamman na samun horo ne a birnin Morogoro, inda kungiyar sa-kai ta APOPO ke aiki tsawon fiye da shekaru 20. Tare da amfani da guda daga cikin hanyoyi mafi kaifin salo na sansana irin na dabbobi, ana shirya wadannan berayen ko gafiyoyi ne da nufin ayyukan ceto rayuka. Horaswar na amfani da tarihin ilmantarwa, irin na gargajiya da kuma na zamani. Sophia Madinda guda ce cikin masu wannan aikin da ta ce, wasunsu sun tsorata da yiwuwar samun nasara a aikin da fari amma kuma daga bisani sun gane yadda gafiyoyin ke da amfani.
Karin Bayani: Cutar Lassa ta halaka mutum 110 a Najeriya
Daya daga cikin muhimman ayyukansu dai shi ne, yaki da tarin fuka da har yanzu ke zaman daya daga cikin cututtuka masu kisa a duniya. Hukumar Lafiya ta Duniya WHO ta ce, cutar ta kashe mutane fiye da miliyan daya da dubu 200 a bara a lokacin da Afirka ke daukar alkaluma mafi yawa. Gafiyoyn APOPO na bincika samfurin majina daga asibitocin Tanzaniyan, domin gano wadanda gwaje-gwaje na yau da kullum suka kasa gano su. Kowanne bera ko gafiya na iya duba samfuri 100, a cikin mintuna 20 kacal.
Tun daga shekarar 2007, wadannan berayen sun gano fiye da marasa lafiya dubu 30 da ke dauke da cutar. Wannan na iya taimakawa, wajen hana yaduwar cututtuka da dama. Duk da nasarorin da suka samu, Hukumar Lafiya ta Duniya ba ta amince da beraye ko gafiyoyin a matsayin kayan gwaji na farko ba. Kowanne samfurin da suka gano dai, dole ne a tabbatar da shi da binciken dan Adam kafin a fara yin magani. Sabon aikinsu yanzu shi ne ceto mutane bayan aukuwar wani bala'i.
Karin Bayani: Cutar zazzabin Lassa ta bulla a kasar Benin
Wasu berayen suna da kankanta sosai, don su shiga tarkacen kasa bayan girgizar kasa. Suna dauke da karamar jakar baya da na'urar amon sauti, domin taimaka wa masu ceto gano wadanda suka makale. Wata kungiya, ta tura su zuwa Turkiyya. Horar da kowace gafiya ko bera dai, na cin kusan Euro 6,000. Amma a tsawon rayuwarsu ta kusan shekaru 10, “berayen jarumai” za su iya sadaukar da mafi yawan lokacinsu don ceto rayuka. Daga share filayen da ke da nakiyoyi zuwa dakile yaduwar cututtuka masu hadari, wadannan jaruman dabbobi suna nuna cewa wani lokaci kanana na iya yin tasiri mai amfani.