ASEAN na taro da China da kasashen Gulf kan harajin Trump
May 27, 2025Shugabannin kasashen yankin kudu maso gabashin nahiyar Asiya sun hallara a birnin Kuala Lumpur na kasar Malaysia a wannan Talata, da nufin lalubo hanyoyin bunkasa tattalin arzikinsu da inganta harkokin kasuwanci da cinikayya, ta hanyar dakile munin tasirin karin harajin da shugaban Amurka Donald Trump ya kakabawa kasashen duniya.
Karin bayani:Shugaban China na matakin karshe na ziyara a Asiya
Wannan ne karon farko da kungiyar ASEAN ke taro da China da kuma kasashen yankin Gulf, wato China and the Gulf Cooperation Council GCC, da suka kunshi kasashen Bahrain da Kuwait da Oman da Qatar, sai Saudi Arebiya da kuma Hadaddiyar Daular Larabawa.
Karin bayani:Kasar Indiya ta dauki matakan diflomasiya a kan Pakistan
Firaministan Malaysia Anwar Ibrahim ya ce wannan wata gaba ce ta tunkarar sabuwar alkiblar fadada alakar kasuwanci a tsakanin makwabtan juna, da suke fatan za ta haifar da alheri marar misaltuwa.