Ana zargin bullar cutar Ebola a Jamhuriyar Czech
May 17, 2025Tuni hukumomi a Jamhuriyar Czech suka dauki mataki na gaggawa sakamakon zargin da ake yi na samun bullar cutar Ebola a kudancin birnin Tabor. Kafofin yada labaran kasar sun ruwaito cewa yanzu haka an killace wani dan asalin Amurka da ya koma kasar daga Kwango a wani asibiti da ke Prague.
Sai dai kuma kafofin ba su fayyace daga Jamhuriyar Dimokradiyyar Kwango ko kuma makwafciyarta Kwango Brazzaville ne mutumin ya je ba. Mutumin mai shekaru 40 da haihuwa ya kai kanshi asibiti ne bayan da ya fara jin alamun ciwo, sai dai kuma likitoci sun ce ana sa ran samun sakamakon gwaje-gwajen da suka yi mishi a wannan Asabar din yayin da ake bincike kansu a nan Jamus.
Cutar Ebola dai na daga cikin cututtuka da suke barazana ga rayuwar jama'a, inda ake iya daukarta daga wani zuwa wani. A shekarar 2013 ne dai cutar Ebola ta bulla a yammacin nahiyar Afirka, wanda ta yi sanadin rayukan mutane 10,000 sama da shekaru uku.