Zaben sabon shugaban Bankin Afirka
May 29, 2025A wannan Alhamis ake sa ran kammala zaben sabon shugaban Bankin Raya kasashen Afirka tsakanin 'yan takara biyar da ke zawarcin kujerar ciki har da mace guda, kuma duk wanda ya samu nasara zai maye gurbin Akinwumi Adesina wanda ya fito daga Najeriya. A zaben shekara ta 2015 shekaru 10 da suka gabata lokacin da Adesina ya samun wa'adin farko na shekaru biyar sai da aka yi zabe gazaye na shida kafin ya samu nasarar.
Karin Bayani: Bankin AfDB ya fusata da rancen da Afirka ke karba
'Yan rahakarar neman shugabancin bankin raya kasahsen na Afirka da ke gaban gaba su ne Amadou Hott tsohon ministan tattalin arzikin kasar Senegal da Sidi Ould Tah tsohon ministan tatatlin arzikin kasar Mauritaniya.
Sannan akwai Samuel Munzele Maimbo masanin tattalin arziki daga Zambiya da Bajabulile Swazi Tshabalala daga Afirka ta Kudu wadda ta rike mataimakiyar shugabar bankin na Afirka kana akwai Abbas Mahamat Tolli, tsohon gwamnan babban bankin kasar Chadi kuma tsohon ministan kudi.
Duk 'yan takara biyar sun yi alkawarin karfafa matsayin bankin na raya kasashen Afirka karkashin manufofin da abankin yake tafiya.