Ana zaben shugaban kasa a Koriya ta Kudu
June 3, 2025Talla
Zabe ne da ke zuwa bayan tsige tsohon shugaban kasar Yoon Suk Yeol da majalaisar dokoki ta yi, tare da ayyana dokar soji a bara.
Manyan 'yan takara dai a zaben na Koriya ta Kudu, su ne madugun adawa mai tsananin ra'ayin gaba da gaba dai, Lee Jae-myung da kuma mai ra'ayin 'yan mazan jiya Kim Moon Soo, da ya fito daga jam'iyyar tsohon shugaban kasar.
Kuri'ar jin ra'ayin jama'a dai na nuna madugun adawa Lee Jae-myung ne ke da rinjaye.
Kasar ta Koriya ta Kudu dai ta fada rudanin siyasa cikin watanni shida, bayan kafa dokar sojin cikin watan Disamba.
Za dai a bayyana wanda ya lashe zaben na yau ne akalla a ranar Laraba.