Ana wasan cin kofin Afirka na mata a Maroko
July 21, 2025Bayan lallasa takwararta ta Faransa da ta yi a bugun daga kai sai mai tsaron gida, a yanzu haka kungiyar kwallon kafa ta mata ta Jamus ta samu nasarar kai wa ga wasan dab da na karshe wato Semifinals a gasar cin kofin zakarun nahiyar Turai wato EUFA Women Champions League. An dai kwashe mintuna 120 ana fafatawa da kunnen doki daya da daya, kafin daga bisani Jamus din ta samu nasara a bugun daga kai sai mai tsaron gida da ci shida da biyar. Za dai a iya cewa 'yan mata na Jamus sun taka rawar gani, ganin cewa Jamus din ta buga mafi akasarin wasan da 'yan wasa 10 ne kacal bayan da aka bai wa 'yar wasanta jan kati wato katin kora a mintuna 13 da fara wasan. Ingila ta lallasa Sweden da ci uku da biyu kana Norway ta sha kashi da ci biyu da daya a hannun Italiya. A yanzu haka dai Ingila za ta fafata a wasan kusa da na karshe da Italiya a Talatar da ke tafe 22 ga wannan wata na Yuli da muke ciki, kana a fafata tsakanin Jamus da Spaniya a ranar Laraba 23 ga watan na Yuli.
Karin Bayani:Gasar FIFA Club World Cup cikin Labarin Wasanni
A gasar cin kofin kwallon kafa ta nahiyar Afirka ta mata WAFCON, inda Najeriya da Ghana da Afirka ta Kudu da kuma Maroko mai masaukin baki suka kai ga wasan kusa da na karshe wato Semi Final.
Harkar dai har yanzu ta mata ce, an kammala gasar cin kofin kwallon kwando ta duniya ta mata 'yan kasa da shekaru 19 a duniya. Najeriya na daga cikin kasashen da suka samu fafatawa a wannan gasa a karo na farko bayan shekaru 20.
Lois Boisson ta samu nasararta ta farko a gasar wasannin kwallon tennis ta French Open, a wasan kusa da na karshe da aka gudanar a birnin Hamburg na Jamus da nasarar da ta samu a kan takwararta Anna Bondar ta kasar Hangarai da ci bakwai da biyar da kuma shida da uku. Mai shekaru 22 a duniya, an fara saninta ne a yayin gasar Grand Slam da aka bayyana ta a matsayi na 361 a jadawalin kwallon tennis din a duniya. A yayin jawabinta na godiya Bajamushiyar, ta nemi a yi mata afuwa domin wannan ne karo na farko da ta samu nasarar da ta ba ta damar yin bayani tare da furta kalmar Danke wato na gode ke nan da Jamusanci ga dandazon masu kallo da magoya bayanta.