Ana shari'ar karshe ta makomar tsige Yoon Suk Yeol
February 25, 2025Tsigaggen shugaban kasar Koriya ta Kudu Yoon Suk Yeol na fuskantar shari'ar karshe kan tsigeshi da aka yi daga karagar mulki a ranar Talata.
Alkalai za su duba tabbatuwar tsigeshi da aka yi ko kuma a'a bayan kafa dokar soji a yayin da ya ke rike da madafun ikon kasar.
Koriya ta Kudu: Shugaba Yoon ya gurfana a gaban kotu
Matakin na mista Yoon ya jefa kasar da ke kan turbar dimokuradiyya cikin rudanin siyasa lamarin da ya sa majalisar dokoki ta tsige shi a watan Disambar 2024.
Tsohon shugaban kasar mai shekara 64 ya na garkame tun bayan damke shi da hukumomi suka yi a watan da ya gabata tare da fuskantar shari'a.
Shugaba Yoon ya ki bayar da kai bori ya hau— Masu bincike
Masu zan-zangar nuna goyon baya ga Yoon din sun hallara a wajen kotun tare da neman a wanke shi daga zarge-zargen da ake masa.
Zaman kotun na Talata shi ne na karshe kafun alkalai takwas su rufe kofa su kuma yanke hukunci kan makomarsa.