Ana neman ganin sojoji sun saki Bazoum
July 23, 2025Kungiyar da ke fafutikar kare hakin dan Adam ta Human Rights Watch (HRW) ta ce hukumomin na mulkin soja a Nijar sun baiwa bangaran siyasa karfi kan batun ci gaba da tsare hambararran shugaban kasar Mohamed Bazoum inda ta ce an yi biris da bangaren doka. Da yake Magana kan tsokacin da na kungiyar ta kasa da kasa mai kula da hare hakin bil-Adama ta HRW ta yi Docta Atto Namaiwa ya ce ana iya kafa dalili bisa dalillai biyu domin duba ingancin sanarwar da kungiyar ta kasa da kasa ta yi kan wannan batu na ci gaba da tsare tsohon shugaban kasa Bazoum da mai dakinsa.
Karin Bayani:Nijar: Ko sakin Bazoum zai saukaka al'amura?
Tun dai a watan Agustan 2023 aka tuhumi tsohon shugaban da aka hambare Mohamed Bazoum da laifuka na cin amanar kasa da katsalandan ga taron cikin gida da ma na waje, wanda kungiyar ta ce bayan nan an samu kiraye-kiraye daga kungiyoyi daban-daban na neman a saki hambararran shugaban kasar da mai dakinsa amma ta ce har ya zuwa yanzu ba a gabatar da shi a gaban wani alkali ba. Amma a cewar Alhaji Oumarou dan Madamin Damagaram mai sharhi kan harkokin da shafi kasashen Afrika, na ganin cewa shi dai wannan batu ne na juyin Mulki ya danganta da yadda su magabatan kasar ke kallon lamarin ganin cewa a baya sun yi magana kan dalillai na tsaro.
Kungiyar ta HRW ta ce ta yi imanin cewa wannan tsarewar da aka dade ba tare da an gurfanar da su a gaban kotu ba, wani bangare ne na murkushe 'yan adawa da kungiyoyin fararen hula kuma ta ce duk kwana guda da Mohamed Bazoum zai yi a tsare na kara nesanta kasar ta Nijar daga tafarki na dimokuradiyya, a cewar Ilaria Allegrozzi, babbar jami'ar bincike ta kungiyar a yankin Sahel.