Ana damuwa kan shirin dakatar da rabon abinci a Nijar
March 11, 2025A cikin wata sanarwa da ta fitar, Hukumar Samar da Abinci ta MDD wato PAM ko WFP ta ce daga watan Afirilun 2025 ne za ta dakatar da bayar da tallafin abincin ga mutane mabukata miliyan biyu, da suka hada da 'yan gudun hijira na cikin gida da sauran mutanen karkara marasa galihu a kasashen Nijar, Mali, Burkina Faso da Najeriya. Sannan wannan mataki zai shafi mazauna yankunan da yaki ya daidaita a Sudan, Chadi da ma 'yan gudun hijirar Mali a Moritaniya.
Karain bayani: Barazanar matsalar jin kai a kasar Nijar
PAM ko WFP ta ce ta dauki matakin ne sabili da rashin kudaden gudanar da aikinta. Hasali ma dai, tana bukatar taimakon miliyan 620 na Dalar Amirka domin iya kai tallafin a wadannan kasashe. Alkassoum Abdourahmane, kwararre a fannin aikin agajin kasa da kasa ya ce za a iya yi fassara daban-daban ma wannan matsala da hukumar MDD ta shiga ta kasa samun kudaden aiwatar da shirin agaji a wadannan kasashe.
Karin bayani: Karancin abinci ya sa Nijar neman agaji
Ko a shekarar da ta gabata ta 20224, PAM ko WFP ta sanar da bayar da agaji kama daga na abinci zuwa na abinci mai gina jiki ga yara da kuma magunguna ga mutane sama da miliyan uku da rabi a kasa Nijar. Wannan ya sa Abou Zeidy Sanoussi Abdoul'Aziz na kungiyar Mojedec da ke gudanar da aikin agaji a Nijar bayyana damuwa a kan matakin dakatar da tallafin abincin. Sannan, shugaban kungiyar ta Mojedec ya yi kira ga gwamnatin mulkin sojan Nijar da ta gaggauta daukar mataki a kai.
Karin bayani: Sahel: Yawaitar yunwa saboda ta'addanci
Sai dai Alkassoum Abdourahmane ya ce akwai bukatar yin garanbawul ga tsarin agajin agajin kasa da kasa a duniya idan ana son magance irin wannan matsala da Hukumar Samar da Abincin ta MDD ta fuskanta. Wannan matakin ya zo ne a daidai loakcin da kungiyoyin agaji na ciki da wajen Nijar suka dakatar da aiki a bisa umurnin gwamnati ko kuma don radin kansu bayan juyin mulki, lamarin da ya jefa ‘yan kasar cikin gararin rayuwa.