SiyasaGabas ta Tsakiya
Isra'ila ta kai sabbin hare-hare kan Iran bayan Amurka
June 22, 2025Talla
Sojojin juyin-juya halin Iran tara na kasar Iran aka halaka sakamakon wani harin Isra'ila a yankin tsakiyar kasar ta Iran, yayin da ake ci gaba da fito na fito tsakanin bangaorin biyu. Tuni mahukuntan Iran suka tabbatar da wannan kisa. Sannan kasar ta tabbatar akwai mutanen da suka jikata sakamakon hare-haren da Amurka ta kaddamar kan cibiyoyin makamashin nukiliyar kasar.
Karin Bayani: Iran ta sha alwashin kare kanta "ta ko halin kaka"
Ita ma kasar Iran ta kaddamar da farmaki kan Isra'ila. Gwamnatin kasar Iran ta kama mutane uku, inda daya ya fito daga Turai bisa zargin leken asiri kamar yadda majiyoyin sharia na kasar suka ruwaito a wannan Lahadi. Iran ta bayyana cewa za ta ci gaba da daukan matakan kare kanta.