Najeriya na fama da karancin ruwa
March 22, 2022Abuja shedkwatar Najeriya na cikin biranen da ke fama da karancin ruwa. Haka lamarin yake a wasu sassan birnin inda akan dauki kwanaki ba tare da samun ruwan famfo ba, musamman a unguwanin da ke gefen birnin, wannan ya sanya mutane da dama komawa ga gina rijiyoyin burtsatse da yawa.
Ruwa akan ce abokin aiki, kuma shi ne rayuwa amma sannu a hankali ruwan ya zama wahala ga mutanen da ke zama a sassan Najeriya da dama, saboda gaza samunsa daga gwamnati da aka dora mata alhakin samar da ruwan ga jama’a.
Wannan ya sanya mutane da dama gina rijiyoyin burtsatse a gidajensu domin samun ruwa, amma ana ganin akwai illolin da hakan ke yi ga kasa. Batun samar da ruwan sha muhimmi ne a kasa irin ta Najeriya, duk da haka al'ummarta na kokawa da karancinsa a yanayi na ga koshi ga kwanan yunwa.