Ana alhinin rasuwar Sheikh Dutsen Tanshi
April 4, 2025Jama'a da dama daga sassa daban-daban ne suka halarci sallar jana'izar marigayin wanda aka gudanar a filin da Dr Idris Dutsen Tanshi ya saba gudanar da sallar idi wato filin Games Village kuma manyan malaman addinin musulunci da kungiyoyi daban-daban sun halarci jana'izar.
Malamin ya rasu ne bayan fama da jinya. Malam Idris ya yi suna a fagen Ilmin Tauhidi wanda har sai da ta kai shi shiga kurkuku.
Bayan fita waje jinyar da tayi ajalinsa, Malam Idris ya dawo Bauchi kwana biyu kafin karamar sallah, inda jama'a suka yi tsammanin shi zai jagorancin sallar idi amma bai samu zarafin hakan ba.
Daga cikin malaman kungiyar izala da suka mika sakon ta'aziyya akwai Sheik Musa Yusuf Asadussunna na jihar Kaduna.
Malam Idris ya rasu yana da shekaru 65. Ya bar 'ya'ya sama da 30 da jikoki da dama. Al'ummar musulmi a jihar Bauchi sun mika sakon ta'aziyyarsu bisa ga wannan rashi da tayi na babban malamin.
Kafin rasuwar Dr Idris, mutum ne da yake haba-haba da 'yan jarida a duk lokacin da aka bukaci hira da shi kamar yadda hirarsa ta karshe da DW ta kara tabbatarwa.