An zargi magugun adawan Tanzaniya da laifin cin amanar kasa
April 10, 2025Talla
Kama shugaban jam'iyyar ta Chadema ya zo ne a daidai lokacin da masu lura da lamuran siyasa, ke zargin gwamnatin shugaba Samia Suluhu Hassan da murkushe 'yan adawa gabanin babban zaben kasar na watan Oktoba.
Wannan dai ba shi ne karon farko da hukumomi ke tsare Lissu ba. Sai dai wannan shi ne karon farko da aka yi masa irin wannan mummunan tuhuma. Tun da farko ‘yan sanda sun ce an yi masa tambayoyi kan zargin tunzura jama'a don hana zaben.
An tsare madugun adawan da wasu ‘yan jam'iyyar ne bayan sun halarci wani taro a Mbinga, wani gari da ke kudancin yankin Ruvuma, inda jami'an 'yan sanda suka harba barkonon tsohuwa domin tarwatsa taron.