SiyasaJamus
Merz ya zama sabon shugaban gwamnatin Jamus
May 6, 2025Talla
Majalisar dokokin Jamus ta Bundestag ta zabi Friedrich Merz na jam'iyyar CDU a matsayin sabon shugaban gwamnati lokacin zabe zagaye na biyu, bayan ya gaza samun kuri'un da yake bukata a zagayen farko na zaben.
Karin Bayani: Jamus: Merz ya gaza samun amincewar majalisa
A zaben Merz ya samu kuri'u 325 na jam'iyyun kawance daga majalisar mai mambobi 630. Kafin zama shugaban gwamnati ana bukatar kuri'u 316 kuma jam'iyyar CDU/CSU da kuma jam'iyyar SPD suna da kujerun majalisar 328, fiye da adadin da ake bukata.