An yi tir da harin Kenya
April 3, 2015Talla
Jama'a a garin Garissa na kasar Kenya na ci gaba da neman 'yan uwa da hari kan jami'a ya ritsa da su a birnin da ke yankin arewa maso gabashin kasar. An tabbatar da mutuwar kusan mutane 150, lokacin da maharan na kungiyar al-Shebaab ta kasar Somaliya suka kai harin.
Shugaba Uhuru Kenyatta ya ce gwamnati tana kara karfafa tsaro domin tunkarar hare-haren 'yan bindiga.
Shugaban Kiristoci mabiya darikar Katolika na duniya Papa-Roma Francis ya yi tir da farmaki na kasar ta Kenya da ya kai ga mutuwar kusan mutane 150, abin da ya kira da aikin rashin hankali mai muni.