An tsaurara matakan tsaro a Abuja gabanin bikin rantsar da shugaban ƙasa a ranar Lahadi
May 26, 2011Talla
Jamia'an tsaron tarayyar ta Najeriya sun ce sun shirya tsab domin kaucewa sake tashin bama-bamai da suka tarwatsa taron bikin ranar 'yancin kan Najeriya a ranar ɗaya ga watan Oktoban da ya gabata. A babban birnin tarayya wato Abuja an tsananta binciken ababan hawa a ciki da kuma wajen birnin musamman motocin dake shiga birnin daga wasu sassa na Najeriyar.
Batun samar da tsaron rayuka da dukiyoyin al'umar ƙasar dai na ɗaya daga cikin manyan ƙalubalen dake gaban sabbin zaɓaɓɓun shugabannin na Najeriya.
A ƙasa mun yi muku tanadin rahotannin wakilinmu daga Abuja Ubale Musa da kuma na jihar Kano Abudurrahaman Kabir waɗanda suka duba mana yadda yanayin harkar tsaro yake a yankunansu.
Mawallafi: Mohammad Nasiru Awal
Edita: Ahmad Tijani Lawal